Mutane goma sha shida ne aka ci tarar su har Riyal dubu goma, daidai da dalar amurka 2,666 sakamakon shiga gurare masu tsarki a Makka ba tare da izini ba, in ji kakakin Hukumar Tsaro ta Al’umma.
Ma’ikatar harkokin cikin gida ta Saudiya ce dai ta hana shiga gurare masu tsarki da sukaMuzdhalif Arafat, Mina da Muzdhalifa ba tare da izini ba daga 28 ga watan Dhul Qadah zuwa 12 ga Dul Hijjah.
Haka kuma za a ninka tarar idan aka maimaita laifin.
Mahukunta sun yi kira ga ƴan ƙasa da su bi dokokin da a ka sanya domin cimma nasara a Hajjin bana.
An shanfiɗa matakan ne domin kariyar alhazai ga kamuwa da annobar COVID-19