Mutum 10,000 ne za su yi aikin Hajji na bana saboda annobar korona
Yayin da ya rage kasa da mako guda a fara gudanar da aikin Hajjin bana a ƙasa mai tsarki, hukumomin Saudiyya na ci gaba da shirye-shirye aiwatar da wannan muhimmiyar ibada bana.
A bana dai mutum 10,000 ne kacal za su yi ibadar kuma mazauna Saudiyya kawai, ciki har da ‘yan ƙasar da kuma wasu da suka je daga ƙetare.
An rage yawan masu zuwa ibadar aikin Hajjin ne saboda annobar korona wadda ta addabi al’ummar duniya.
Tuni dai mahukunta a Saudiyya suka fitar da wasu sharuda guda takwas ga mahajjatan na bana, sharudan kuwa sun hadar da:
- Dole ne duk wanda zai yi aikin Hajjin na bana ya kasance ba shi da ciwon siga.
- Dole mahajjata su kasance ba su da lalurar hawan jini.
- Dole mahajjata su kasnace ba shi da wata lalura da ta shafi zuciya.
- Dole mahajjata su kasance ba su da wani ciwo ko lalura da ta shafi numfashi.
- Ya kasance mahajjata ba su kamu da cutar korona ba ko kuma sun yi a baya.
- Shekarun mahajjaci dole su kasance tsakanin 20 zuwa 65.
- Dole mahajjata su kiyaye da dokokin da ma’aikatar lafiya ta Saudiyya ta gindaya don kariya daga cutar korona, ma’ana dole su kiyaye da dokar killace kai mako biyu kafin aikin Hajji da kuma mako biyu bayan kammala aikin Hajji.
- Sannan ya kasance dukkanin Alhazai da Hajiyoyin bana ba su taba yin aikin Hajji ba.
Daga BBC Hausa