DA ƊUMI-ƊUMI: An kama alhazan bogi 244 a Makka

0
424

 

Jami’an tsaro sun cafke mutane 244 ranar Talata yayin da suke ƙoƙarin shiga wurare masu tsarki na yin ibadar Hajji domin yin ibadar tare da karya sharuɗɗan kariya da kamuwa da annoba.

 

Tuni dai aka ɗauki matakan hukunci a kan su bayan an samu dukkanin shaidu a kan su, Kamfanin Dillancin Labarai na Saudiya be ya rawaito ta bakin Mai magana da Yawun Jami’an tsaro na al’umma.

 

Mai magana da yawun hukumar ya yi kira ga duk ƴan ƙasa da baƙi da su kiyaye sharuɗɗan da a ka gindaya domin yin aikin Hajji da kuma gujewa shiga gurare masu tsarki ba tare da izni ba.

 

“Jami’an tsaro sun sanya matakai masu tsauri a gurare masu tsarki kuma an tanadi hukunci ga masu kunnen ƙashi” in ji shi.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here