Sallah:? Mun yi alƙawarin yin kyakyawan shiri a Hajjin 2021- Shugaban NAHCON

0
391
Daga Mustapha Adamu
Shugaban Hukumar Hajji ta Ƙasa, NAHCON, Barista Zikrullah Kunle Hassan ya yi alƙawarin samar da duk wasu hanyoyi da za su sanya shirin Hajjin 2021 ya zama mai cikakken nasara.
Shugaban ya yi alƙawarin ne a saƙon sa na barka da sallah da ya aikewa ɗaukacin musulmin Najeriya a wata sanarwa da ya sawa hannu da kan sa ranar Juma’a.
Ya ce hukumar za ta tabbatar ta tanadi kyawawa kuma ƙwararan matakai don ganin ta yi shiri mai cike da nasarori ga alhazai da sauran mash ruwa da tsaki a harkar Hajji.
Barista Hassan ya nusar da cewa halin ƙunci da firgici da duniya ta tsinci kan ta ya cancanci a yi yanka domin Allah ya yaye mana.
Ya ce yanka ne da miliyoyin musulmai za su so su yi shi yayin da suke kan dutsen Arfa, amma sai wata ƙwayar cuta da ba a iya ganin ta, ta hana wajen musulmai miliyan 2.5 zuwa aikin Hajjin bana. 
Daga nan sai ya roƙi Allah da Ya sanya a samu a yi aikin Hajjin baɗi, sannan ya yi addu’a ga alhazan da ke ƙasa mai tsarki su ke yin aikin Hajjin bana.
“Yayin da mu ke bikin babbar sallah, su kuma alhazai waɗanda Allah Ya bawa ikon yin aikin Hajjin bana Allah Ya karbi ibadun mu baki ɗayan mu.
“Allah Ya karbi hajjin su sannan mu kuma Ya buɗe mana hanya mu samu damar yin aikin Hajjin 2021.” in ji shi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here