Hajjin 2020: Alhazai sun cire harami bayan kammala rukunnan aikin Hajji

0
573
A ranar Juma’a ne Alhazai suka kammala rukunnan aikin Hajj guda huɗu, wanda yayi daidai da 10 ga watan  Dhulhijja, wacce kuma a ke kira da Yaum Al -Nahr, wato ranar yanka lokacin da musulmai ko da ba aikin Hajji suke ba a faɗin duniya suke bikin Eid Al-Adha.
Bayan sun isa Minna daga Muzdalifah sai alhazai su zarce zuwa Jamrat  Al-Alaqba, wato wajen jifan shaiɗan, su yi yanka sannan su cire  sannan su aske gashin kan su ko su rage shi, sannan mata su yanki jelar gashin kan su tsawon tsawon ɗan yatsa. Daga nan sai alhazai su canja zuwa kayan su da suka saba sakawa.
Daga nan sai alhazai su zarce zuwa Makka inda za su yi Tawaf Al-ifada da kuma sa’ayi, wato safa da marwa, wasu jiga-jigan hajji guda biyu.
Alhazan da su ka yi sa’ayi tare da Ɗawaful Qudum, wato Ɗawafin Sauka a Makkah, to sai sun sake yin wani sa’ayin.
Daga nan sai su cire harami gaba ɗaya. A ragowar kwanaki 3, waɗanda a ke kira da Ayyamul Tashreek, aikin kawai da ya rage shine jifan shaiɗan a ɗaya daga cikin waɗan nan dutsunan na Jamra da ake kira Jamratul Sughra, Jamratul Wusɗa da Jamratul Aqba sau 7 bayan sun yi zama na kwanaki 3 a Minna.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here