Alhazai za su killace kawunan su bayan kammala Hajjin 2020 ran Lahadi

0
283
Daga Mustapha Adamu
A ranar Lahadi ne aka kammala aikin Hajjin bana bayan da alhazai suka yi ɗawafin bankwana a masallacin harami na Makka.
Daga nan kuma sai alhazai su killace kawunan su a wani mataki na biyayya ga sharuɗɗan kariya daga cutar coronavirus.
Tun sanyin safiyar Lahadi ne dai alhazan suka ɗauki hanyar yin jifan sheɗan karo na uku kuma na ƙarshe, kamar yadda Mataimakin Ministan Ma’aikatar Hajji da Ummara, Dakta Abdulfatah Al-Mashat ya yi bayani.
Daga nan kuma sai su zarce zuwa Minna, sa’an nan bayan ƙarfe 4 na yamma, sai su wuce zuwa Harami na Makka domin yin ɗawafin bankwana.
Daga nan kuma sai a yi musu gwajin cutar corona bayan sun kammala duk ayyukan da ke cikin Hajji kafin su bar birnin Makka, in ji shi.
A ranar Asabar ne dai a ka fara jifan sheɗan ɗin cikin ƙwaƙƙwaran tsaro da kuma matakan kariyar lafiya.
Mahukunta sun tabbatar an bi dokar bada tazara da juna sannan kuma a ka bawa kowanne alhaji kyautar kayayyakin alato iri-iri daga Ma’aikar Hajji da Ummara a narar idi.
Haka zalika a ranar Asabar ɗin ne a ka ci gaba da yiwa Masallacin Harami feshin magani inda a ninka feshin har sau goma a rana.
Haka kuma Ma’aikatar Lafiya ta Saudiya ta bayyana cewa babu wani Alhaji da a ka samu da cutar ta corona a cikin alhazan da suka yi aikin Hajjin bana.
Matakan kariyar da gwamnatin ta ɗauka sun haɗa da yin gwajin cutar, lura da kai-komo ɗin su ta hanyar na’urar da ake maƙalawa a hannu sannan da kuma umartar alhazan da su killace kan su kafin da kuma bayan kammala aikin Hajji.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here