Hajjin 2020: Za a fara maidawa maniyyata kuɗaɗen su a Katsina

0
378

 

Daga Mustapha Adamu

Gwamnan Jihar Katsina, Aminu Bello Masari, ya yarje da a maidawa maniyyatan jihar kuɗaɗen su da suka ajiye domin zuwa Hajjin 2020.

Shugaban Hukumar kula Da jin daɗi da Walwalar Alhazai ta Jihar, Alhaji Suleman Nuhu Kuki ne ya bayyana hakan yayin ganawa da manema labarai a ofishin sa ranar Litinin.

Ya ce waɗan da kuma suke da niyyar su bar kuɗaɗen nasu har zuwa Hajjin 2021 za su iya yin hakan amma a ƙarƙashin yarjejeniya da Hukumar wacce yanzu take shirin fara rijistar Hajjin baɗi.

Kuki ya ƙara da cewa nan ba da daɗewa ba za a fara biyan kuɗaɗen ga maniyyatan da suka nema, in da waɗanda suke da niyyar ajiyewa sai Hajjin baɗi su tuntubi ofisoshin shiyyoyin su domin cike takardar neman ci gaba da ajiye kuɗaɗen.

Alhaji Kuki ya shidawa manema labaran cewa lokacin da aka dakatar da karbar biyan kuɗaɗen aikin Hajjin 2020, hukumar ta karbi kuɗaɗen maniyyata 1,539 da suka biya kuɗaɗen nasu da ya fara daga N300,000 zuwa N1,500,000.

“Kamar Hukumar Hajji ta Ƙasa, NAHCON, muma a nan Katsina, da maniyyatan mu mun karbi soke aikin Hajjin bana da kyakkyawar niyya da kuma yadda da ƙaddara.

“Ya godewa gwamnatin Katsina a bisa gagarumar gudunnawar da ta ke bawa hukumar, da kuma NAHCON sabida shawarwari da jagoranci sannan sai maniyyatan jihar sakamakon hakuri da juriya da suka nuna a wannan mawuyacin hali da muke ciki,”

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here