COVID-19: IHR ta yabawa Saudiyya kan yin Hajjin 2020 cikin nasara

0
299

 

Ƙungiyar Masu Rahotannin Aikin Hajji Mai Zaman Kanta, wacce a ka fi sani da Independent Hajj Reporters (IHR), ta taya Saudi Arebiya, ƙarkashin jagorancin  Hadimin Masallatan Hatami biyu Masu Tsarki, Sarki Salman Bin Abdulaziz da kuma Yarima Muhammad Bin Salman a bisa aiwatar da Aikin Hajjin bana cikin nasara duk da annobar COVID-19.

 

A wata sanarwa mai ɗauke da sa hannun Shugaban ƙungiyar na ƙasa, Ibrahim Muhammad ta ce, a wata wasiƙar yabawa da ta aikewa ƙasar ta hannun Ministan Hajji da Ummara, Mohammed Saleh Bin Taher Benten, ta ofoshin jakadancin ƙasar.

 

Sanarwar ta bayyana cewa, wasiƙar ta ce “mun rubuta wannan wasiƙa ne domin mu taya Saudi Arebiya, ƙarkashin jagorancin  Hadimin Masallatan Hatami biyu Masu Tsarki, Sarki Salman Bin Abdulaziz da kuma Yarima Muhammad Bin Salman a bisa aiwatar da Aikin Hajjin bana cikin nasara duk da annobar COVID-19.

 

Sanarwar ta ƙara da cewa, “bayan ya ƙarbi wasiƙar, Jami’in Hulɗa da Jama’a na ofishin jakadancin, Al Fawzan ya yabawa IHR sannan yayi alƙawarin isar da saƙon wasiƙar zuwa ga Ministan.”

 

A wasiƙar, IHR ta nuna godiya mai yawa ga Hukumar Hajji da Umara ɗin, da sauran hukumomi, ɗaiɗaikun mutane da rukunnai  da suka yi aiki ba dare ba rana har sai da Hajjin bana ya kammala cikin nasara.

 

Ta kuma bayyana cewa nasarar ta kasance abin farin ciki ga ɗaukacin al’ummar musulmai a faɗin duniya.

 

Haka kuma, tun a baya  Shugabanni na duniya suka taya Sarki Salman murnar yin aikin Hajjin bana gami da wani shiri wanda ba a taba irin sa ba sakamakon annobar coronavirus.

 

Ya kamata a sani cewa tun daga farkon aikin Hajji har zuwa ƙarshen ta amma ba a samu wani wanda ya kamu da cutar COVID-19  ɗin ba.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here