Hajjin 2020: Maniyyata 46 ne cikin 1,169 suka nemi a maido musu da kuɗaɗen su

0
544

 

Daga Mustapha Adamu

 

 

Maniyyata 46 a cikin 1,169 da suka biya kuɗin ajiya na Hajjin bana ne suka nemi a maido musu da kuɗaɗen su, kuma tuni aka maidawa kowa haƙƙin sa a cikin su.

 

Shuguban Hukumar kula da Jin Daɗi da Walwalar Alhazai ta Jihar Adamawa, Mallam Salihu Abubakar ne ya bayyana hakan a wajen wani taro, inda ya ce maniyyata 46 ɗin sun nemi a maido musu da kuɗaɗen su ne bayan da hukumomin Saudiya suka yanke hukuncin soke aikin Hajji ga ƴan ƙasashen waje sakamakon annobar COVID-19 da ta tilasta kulle.

 

Ya ƙara da cewa hukumar ta zagaya dukka ƙananan hukumomi 21 inda ta gana da masu ruwa da tsaki ta kuma faɗakar da maniyyatan a kan su bar kuɗin nasu sai su je Hajjin 2021 ko kuma su aika neman a dawo musu da kuɗaɗen su, sai wasu daga cikin su suka nemi a maidowa musu da haƙƙunan nasu.

 

Mallam Abubakar ya kuka bayyana cewa hukumar ta karbi kuɗaɗen ajiya daga maniyyata a bana da adadin su ya haura naira biliyan ɗaya, inda ta zamto wacce ta fi karbar kuɗaɗen ajiya ga NAHCON.

 

Ya kuma nuna cewa a halin yanzu, hukumar ta dakatar da maida kuɗaɗen ga maniyyata har sai bayan Hajjin 2021.

 

Ya kuma yabawa da jinjinawa maniyyatan na Hajjin 2020 da a ka soke a bisa juriya, haƙuri da fahimta da suka yi  a kokacin soke Hajjin.

 

Shugaban ya kuma tabbatarwa waɗanda suka bar kuɗaɗen su har zuwa Hajjin baɗi cewa kuɗaɗen su ba za su salwanta ba.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here