NAHCON ta miƙawa NBTE takardar neman sahalewar kafa Cibiyar Horaswar Aikin Hajji

0
396

 

 

Daga Mustapha Adamu

 

 

Hukumar Hajji ta Ƙasa (NAHCON) ta miƙawa Hukumar Ilimin Fasahohi ta Ƙasa (NBTE) takarda mai ɗauke da buƙatar ta sahale mata ta kafa Cibiyar Horaswa kan Aikin Hajji ta Ƙasa.

 

Shugaban NAHCON, Barista Zikrullah Kunle Hassan ne ya miƙa takardar ga Babban Sakataren NBTE ɗin, Dakta Masud Adamu Kazaure a ofishin sa a yau ɗin nan.

 

Yayin da yake jawabi, Shugaban NAHCON ɗin ya nuna cewa Hukumar na kaikawo domin samar da aikace-aikace iri daban-daban saboda tana aiwatar da kusan dukkan aikace-aikacen ta ta hanyar ƙwarewa.

 

“Muna son mu bawa mutane horo. Muhaɗa tare da nazari a kan ƙididdiga. Mu samar da kundi sannan mu samar da wani mataki ga waɗanda suke da niyyar yin aikin Hajji. Muna son mu bada gudunmawa wajen bunƙasa tattalin arziƙin ƙasa,”

 

Shugaban ya ƙara da cewa NAHCON na da ƙudurin wallafa littafai, ƙasidu da faifayen bidiyo domin bunƙasa tsare-tsaren aikin Hajji.

 

A nasa jawabin, Babban Sakataren NBTE ɗin ya yabawa NAHCON a bisa wannan hobbasar , inda ya kuma tuna cewa Hukumar ta taba kai masa ziyara ofishin sa a Abuja.

 

Ya kuma bayyana irin sharuɗɗa da matakai da za a bi a kafa cibiyar horawar ta aikin Hajji wacce a ke sa ran za ta kawo sakamakon da a ke buƙata.

 

Ya kuma bawa NAHCON shawarar ta canja sunan cibiyar zuwa Cibiyar Horas da Alhazai domin a haɗa da wasu aikace-aikace na alhazan addinin kirista.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here