Saudiya na gagarumin shirin buɗe Ummara

0
405

  

Babban ofishin Shugabancin kula da Harkokin Masallatan Harami Biyu da 

Hukumar Hajji da Ummara ta Saudi Arebiya sun sanar da cewa gagarumin shiri yayi nisa domin buɗe Ummara ta bana, da ta haɗa da ta Ramadan, da kuma shirye-shiryen Hajjin 1442.

 

A wata sanarwa ta haɗin gwiwa da suka fitar, hukumomin sun bayyana cewa an samu nasarori a Hajjin bana, inda kakakin hukumar ya bayyana cewa nan da makonni biyu za su fitar da rahoto a kan darussan da a ka koya a lokacin aikin Hajji.

 

Tun da fari, babban ofishin ta fitar da wani cikakken tsari da za a yi a Harami idan an buɗe yin ɗawafi da Ummara, inda za a yi shirin a gwadaben matakan kariya.

 

Matakan sun haɗa da tantance masallata, raba gurin shiga da fita daga masallacin, faɗaɗa ƙofofin King Abdallah da King Fahad da kuma sanya hatabar ta riƙa ɗaukar ƙasa da kashi 40 na masallata.

 

Za a bayyana waɗan nan matakan ne har sai an ga raguwar annobar COVID-19 a ƙasar da kuma sauran ƙasashe.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here