… Ya nemi goyon bayan hukumar kan ƙudirin kafa Cibiyar Adashin gata domin aikin Hajji
Daga Mustapha Adamu
Shugaban Hukumar Hajii ta Ƙasa (NAHCON), Alhaji Zikrullah Kunle Hassan ya nemi goyon bayan sanun nasarar ƙudirin sa na kafa Cibiyar Horaswa kan Aikin Hajji (HTI) da kuma Adashin Gata kan Aikin Hajji (HSS).
Ya miƙa buƙatar goyon bayan ne yayin da ya kai ziyara zuwa Hukumar Jin Daɗi da Walwalar Alhazai ta Jihar Kaduna, a ofishin ta dake Titin Katsina ranar 19 ga Agusta, 2020.
Alhaji Zikrullah ya bayyana cewa ziyarar ta godiya sakamkon saukar girma da hukumar ta yiwa tawagar NAHCON ɗin duk da an bata sanarwa a ƙurarren lokaci.
A sanarwa mai ɗauke da sa hannun Fatima Sanda Usara, Shugabar Fannin Harkokin Jama’a ta NAHCON, Alhaji Zikrullah ya bayyana cewa maƙasudin ziyarar domin haɗin kai ne wajen tabbatar da ƙudirorin guda biyu daga wajen hukumomin alhazai na jiha waɗanda sune ƙashin bayan wayarwa da al’umma kai a kan hakan.
Shugaban NAHCON ɗin ya fahimci cewa hukumomin jin daɗin alhazai na jihohi ne za su fi amfana da tsare-tsaren biyu idan sun tabbata tunda sune zuke da alaƙa kai tsaye da alhazai da ma’aikata waɗanda sune za su ci gajiyar horaswa kan horaswa a kan yin aikin Hajji da kuma tafiyar da harkokin sa.
A game da Adashin Gata kuwa, Shugaban ya nuna ƙwarin gwiwar sa a kan nasarar tsarin kasancewar sa ya kawo cigaba a masana’antar aikin Hajji kuma dole ne a ƙara ƙarfafa shi.
Shugaban ya ƙara yin bayani a kan Cibiyar Horaswa kan Aikin Hajji, inda ya ce za a kafata ne domin ƙara ƙwarar da harkar aikin Hajji a Nijeriya, bada damar samun ayyukan yi da kuma bunƙasa tattalin arzikin ƙasa.
A nata jawabin, Shugabar Hukumar jin Ɗadi da Walwalar Alhazai ta Kaduna, Hajiya Hannatu Zailani, ta yi alƙawarin taimakawa NAHCON a kan duk wata buƙatar ta idan ta taso saboda ɗumbin shirye-shirye na cigaba da hukumar ta samar.
Ta suffanta ƙudirori biyun da abubuwa ne fa za su haifar da jin daɗi da shauƙi, inda ta nuna alla-alla su tabbata.
Ta kuma sanar da tawogar cewa a cikin maniyyata 2,383 da suka biya kuɗaɗen su domin zuwa Hajjin 2020 da bai yiwu ba, mutane 172 ne kawai suka nemi da a maido musu da kuɗaɗen su.
Ta bayyana cewa da zarar hukumar ta karbi umarnin gwamnati, to za ta fara maidawa waɗanda suka nema haƙƙokin su. Daga ƙarshe kuma Hajiya Hannatu ta gidewa Shugabancin NAHCON abisa ziyarar da suka kawo, inda tayi fatan su koma Abuja lafiya.