Daga Mustapha Adamu
Hukumar Jin daɗi da Walwalar Alhazai ta Jihar Katsina ta fara maidawa maniyyata kuɗaɗen su da suka ajiye domin Hajjin 2020 bayan sun nemi a maido musu da kuɗaɗen nasu.
Da yake jawabi a yayin taron ƙaddamarwa a ofisoshin shiyoyin alhazai guda biyu da suka haɗa da Funtuwa da Malumfashi, Shugaban Hukumar, Alhaji Suleman Nuhu Kuki ya bayyana cewa Gwamna Aminu Bello Masari ya yarje da a biya kuɗaɗen kamar yadda Hukumar Hajji ta Ƙasa ta bada umarni.
Ya ce ana maida kuɗaɗen ne ga maniyyatan da suka biya kuɗaɗen ajiya domin Hajjin 2020 da a ka soke kuma suka nemi da a maido musu da haƙƙoƙin su.
Alhaji Kuki ya kuma yi kira da maniyyatan da suka yarda da su cigaba da ajiye kuɗaɗen nasu domin Hajjin 2021 da su je ofisoshin alhazai na shiyoyin su domin cike takardar yarjejeniya da hukumar ta samar.
Tun a farko, a nasa jawabin, Shugaban kwamitin tantancewar, Alhaji Usman Dalhatu, kira yayi ga maniyyatan da sugar nemi a maido musu da kuɗaɗen nasu da su kawo rasitin su na biyan kuɗin domin sauƙaƙa tsarin biyan.
Sanarwa mai ɗauke da sa hannun Jami’in Hulɗa da Jama’a na hukumar tabbayyana cewa maniyyatan da suka nemi a maido musu da kudaɗen su sun nuna farin ciki a bisa amana da hukumar ta nuna musu