NAHCON ta yabawa Hajj Reporters bisa ƙwazo wajen yaɗa ayyukan ta

0
382

 

 

Daga Mustapha Adamu

 

 

Hukumar Hajji ta Ƙasa (NAHCON) ta yabawa Ƙungiyar Masu Ɗauko Rahoton Hajji Mai Zaman Kanta, da aka fi sani da Independent Hajj Reporters a bisa ƙwazon ta na yaɗa ayyukan hukumar a ciki da wajen Nijeriya.

 

Ƙungiyar Masu Ɗauko Rahoton Hajji an yi mata rijista a natsayin mai zaman kanta kuma ba ta neman kuɗi ba, wacce take ɗauko rahotanni kan aikin Hajji a Nijeriya da Saudi Arebiya.

 

A wasiƙa mai ɗauke da sa hannun Shugaban NAHCON, Batista Zikrullah Kunle Hassan da kwanan watan 18 ga Agusta, 2020, ta ce “Na rubuta wannan wasiƙa ne a mamadin rukunin masu tafi da al’amura, shugabanni da ɗaukacin ma’aikatan NAHCON domin na nuna ɗumbin godiya a bisa kyakkyawar alaƙar dake tsakanin hukumar mu da taku,”

 

Shugaban NAHCON ɗin ya ƙara da cewa, ” Ɗauko tahotanni da kuke yi na nusamman a kan ayyukan NAHCON a ciki da wajen Nijeriya ya bada gagarumar gudunmawa wajen sanar da al’umma a kan irin ayyukan NAHCON,”

 

Babbar hukumar kula da Hajjin ta ƙasa ta kuma ci alwashin ƙarfafa danƙon zumuncin dake tsakanin ta da sauran masu ruwa da tsaki a harkar Hajji da Ummara.

 

Daga ƙarshe kuma hukumar ta baiwa ƙungiyar kyautar kwando a wani mataki na nuna godiya da jin daɗi ga ƙungiyar.

 

Shugaban ya ƙara da cewa gudunmawar da Hajj Reporters ɗin ta bayar wajen nasarorin da NAHCON ta samu tsawon shekaru ba zai musaltu ba.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here