Hajj 2020: Sama da kashi 90 na maniyyata basu nemi a dawo musu da kuɗaɗen su ba

0
9

 

 

Shugaban Hukumar Hajji ta Ƙasa (NAHCON), Barista Zikrullah Kunle Hassan ya bayyana cewa sama da kashi 90 cikin 100 na maniyyatan da suka biya kuɗin ajiya basu nemi a dawo musu da kuɗaɗen nasu ba.

 

Shugaban ya bayyana haka ne lokacin da ya kai ziyarar aiki a Ilorin, Jihar Kwara.

 

Kunle Hassan ya ƙara da cewa kashi 10 ne kacal na waɗan da suka biya kuɗaɗen aikin Hajjin suka nemi a maido musu ds haƙoƙin su bayan da gwamnatin Saudi Arebiya ta soke Hajjin ga ƴan ƙasashen waje sakamakon annobar corona.

 

“Sama da kashi 90 ne suke ds kuɗaɗe a gurin mu kuma bamu san nawa za su cika suyi aikin Hajjin 2021 ba.”

 

Shugaban ya ƙara da cewa dukkanin kuɗaɗen maniyyatan suna nan a ajiye a babban bankin ƙasa, wato CBN.

 

Hassan ya ƙara da cewa NAHCON na aiki hannu da hannu da Hukumomin kula da Jin daɗi da Walwalar Alhazai na Jihohi kan yadda za a rage yawan kwanakin da alhazai suke yi a Saudiya lokacin Hajji domin rage wahalar tafiyar.

 

Ya kuma gargaɗi maniyyata kan zuwa aikin Hajji ta kamfanonin jigilar alhazai na bogi.

 

A nasa bangaren, Shugaban Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta Jihar Kwara, Alhaji Mohammed Tunde Jimo nuna farinciki da ziyarar yayi, inda ya nuna cewa ziyarar ta ƙar danƙon zumuncin dake tsakanin hukumomin biyu.

 

Haka kuma Shugaban kwamitin gudanarwar Hukumar Alhazan ta Kwara, Dakta Sambo Sambaki ne ya ja tawogar baƙin zuwa duba ayyuka a sansanin alhazai da ke Ilorin ɗin.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here