An maidowa maniyyata 423 sama da naira miliyan 440 a Kano

0
230

 

 

Daga Mustapha Adamu

 

Hukumar Kula da Jin daɗi da Walwalar Alhazai ta Jihar Kano ta ce ta maido da sama da naira miliyan 440 ga maniyyatan da suka biya kuɗaɗen aikin Hajjin 2020.

 

A tuna cewa Saudi Arebiya ce ta soke aikin Hajji ga ƴan ƙasashen waje sakamakon yaɗuwar cutar corona, inda mutum 10,000 ne kacal kuma mazauna ƙasar suka samu damar yin ibadar ta bana.

 

Shugaban hukumar, Muhammad Abba Ɗambatta ne ya bayyana hakan a wata ganawa da yayi da kamfanin dillancin labarai na ƙasa, NAN.

 

Shugaban ya bayyana cewa hukumar ta maido naira miliyan 440 ga maniyyata 423 da suka nemi a maido musu da kuɗaɗen nasu.

 

Ɗambatta ya ce adadin maniyyata 1,794 ne suka yi rijistar zuwa aikin Hajjin daga Jihar Kano.

 

“Maniyyata 423 daga cikin wannan adadin ne suka nemi a maido musu da kudaɗen su kuma tuni aka biya kowa daga cikin su. Sauran maniyyata 1,371 kuma sun yanke shawarar ci gaba da ajiye kudaɗen su domin Hajjin 2021,”

 

Ɗambatta ya ƙara da cewa an biya kuɗaɗen ne a ɗaukacin Ƙananan Hukumomi 44 na jihar.

 

Ya  kuma yi kira ga sayran maniyyata da ke da sha’awar karbar kuɗaɗen nasu da su nema ta ofisoshin alhazai na Ƙaramar Hukumar su

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here