Hukumar Jin Daɗi da Walwalar Alhazai ta Jihar Gombe ta kammala maidawa maniyyatan da suka nemi a maido musu da kuɗaɗen su daga Ƙananan Hukumomi 11.
Shugaban hukumar jin daɗin alhazan jihar, Alhaji Sa’idu Hassan ya bayyana cewa maniyyata 1,077 ne suka biya kuɗin aikin Hajji amma 146 ne suka nemi a maido musu da kuɗaɗen su, inda sauran suka amince da su cigaba da ajiye kuɗaɗen su domin aikin Hajjin 2021.
Ya ƙara da cewa waɗanda suka bar kuɗaɗen nasu su za a fara yiwa rijistar aikin Hajjin baɗi.
Shugaban ya kuma sanar da cewa a ranar 9 ga watan Satumba za a fara karbar kuɗaɗen ajiya na aikin Hajjin 2021 kamar yadda Hukumar Hajji ta Ƙasa, NAHCON ta bada umarnI