Hukumar Hajji ta Ƙasa (NAHCON) ta ce ta bijiro da wani sabon tsari na tara kuɗin tafiya aikin Hajji ga masu ƙaramin ƙarfi, wato adashin gata.
Shugaban Hukumar Hajji ta Ƙasa, Barista Zikurullah Kunle Hassan ne ya faɗi hakan a lokacin da ya kaiwa Mai Marta Sarkin Kano, Alhaji Aminu Ado Bayero ziyarar sanya albarka a bisa ayyukan da zai gabatar a Jihar Kano.
Zikirullah Hassan, ya ƙara da cewa hukumar ta samar da asibiti wanda za’a riƙa duba Alhazai tare da Otal bisa tsarin Islama.
Ya kuma cigaba da cewa NAHCON za ta samar da Cibiyar Horo kan sanin makamar aikin Hajji ga dukkan wadanda zasu jagoranci Alhazai.
Da ya ke jawabi, Babban Sakataren Hukumar jin Daɗin Alhazai ta Jihar Kano Muhammad, Abba Muhammad Danbatta, ya godewa Shugaban Hukumar Hajjin ta Ƙasa a bisa ziyarar aiki ta kwanaki biyu da ya kawo Jihar Kano.
Ya ce ziyarar ta zo a daidai lokacin da ake buƙatar ta, inda ya jinjinawa hukumar bisa yadda ta kammala aikin aisibiti mai gadaje 500, da Kuma Otal zuwa kashi 90 na matakin ginin, inda ya ce duka an yi su ne domin Alhazai.
Da ya ke nasa jawabin, Mai Martaba Sarkin Kano, wanda Sarkin Shanun Kano, Alhaji Shehu Muhammad Ɗankadai ya wakilta ya ce “masarautar Kano za ta ci gaba da baiwa NAHCON goyon baya ako da yaushe.
Ya Kuma buƙaci Shugaban Hukumar da ya yi duba na tsanaki akan harkar sauyin kuɗaɗen waje, inda yace “sune suke dagula komai”.
Barista Hassan na tare da kwamishinonin shiyoyi 6 na hukumar.