Dalilin ziyarar mu zuwa jihohi- Shugaban NAHCON

0
252

Daga Mustapha Adamu

Shugaban Hukumar Hajji ta Ƙasa(NAHCON), Barista Zikrullah Kunle Hassan ya bayyana cewa ziyarar da hukumar ke yi zuwa wasu jihohin nijeriya domin ƙulla kyakyawar alaƙa da kuma duba wasu ayyukan da hukumar ke yi a faɗin ƙasa ne.

Wata sanarwa da Shugaban Sashin Harkokin Jama’a, Fatima Sanda Usara ta fitar ranar Juma’a ta ce shugaban ya samu rakiyar manyan kwamishinoni na din-din-din guda uku, daraktoci da kuma wasu manyan ma’aikata na hukumar.

Ta ƙara da cewa a duk jihar da tawogar ta ziyar ta sai ta kai ziyarar girmamawa ga gwamnatin jihar da kuma masarautun gargajiya domin neman tabaraki da kuma goyon baya a bisa kyawawan ayyuka da tsare-tsare da NAHCON ɗin ta bijiro da su. 

 A faɗin Fatima Usara, duk jihar da shugaban ya kai ziyara sai ya nemi goyon bayan shugabanni kan sabon tsarin da ya bijiro da shi na Adashin Gata na zuwa aikin Hajji da kuma Cibiyar Horaswa kan Sanin Makamar Aikin Hajji.

Ta ƙara da cewa Shugaban ya ƙara bayyana cewa daga cikin manyan ƙudirorin hukumar shine rage yawan kwanakin da alhazai suke yi a ƙasa mai tsarki.

Ya kuma alƙawarta sauƙaƙa farashin zuwa aikin Hajji ga kowa ta wasu tsare-tsare da kuma mai jigilar aikin ta zamto ta na’ura mai ƙwaƙwalwa.

Duk da ya nuna cewa ƙudirorin nan na da wuyar aiwatarwa musamman bangaren kuɗaɗen aikin Hajji, duba da cewa farashin ya dogara ne a kan canjin kuɗaɗen ƙasashen waje, Shugaban ya ci alwashin sauƙaƙa farashin aikin Hajji ga duk wani musulmin Nijeriya.

Ya ƙara da cewa hanya mafi gaggawa da sauƙi ta tabbatar da hakan itace Adashin Gata na Aikin Hajji.

A ta bakin shugabannin, sun yabawa tawogar a bisa ziyarar da suka kawo da kuma irin tsarin jagorancin hukumar.

A ta bakin Gwamnan Jihar Jigawa, Muhammadu Badaru Abubakar ya bayyana ƙwarin gwiwar cewa ba dan an soke aikin Hajji ga ƙasashen waje ba da farashin aikin Hajjin 2020 yayi sauƙi .

Haka shima Mai Martaba Sarkin Dutse, Alhaji Muhammadu Nuhu Sanusi ya bayyana jin daɗin sa ga tsarin Adashin Gata na Hajji, inda ya nuna cewa bai kamata gwamnati ta riƙa kashe kuɗaɗe kan aikin Hajji ba.

IHRHausa ta rawaito cewa tawogar ta ziyarci Gwamnoni da Sarakunan Jihohin Bauchi,Kwara,Jigawa,Kano da Katsina.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here