Shugaban Hukumar Alhazai ta Jihar Niger, Alhaji Umar Makun Lapai ya suffanta Hajj Reporters da ƙungiya wacce sanin da a ka yi mata ya wuce iya Najeriya.
Alhaji Makun ya faɗi hakan ne kokacin da ya karbi tawogar shugabannin ƙunNjger, a bisa jagorancin shugaban ta na ƙasa, Ibrahim Muhammad a Minna, Jihar Njger ranar Laraba.
Shugaban hukumar ya kuma yabawa IHR a kan irin rawar da take takawa wajen ƙara ƙawata harkokin aikin Hajji ta hanyar faɗakar da al’umma kan jigilar aikin Hajji.
Tun a farko, Shugaban ƙungiyar, ya bayyana cewa yayi aiki da Alhaji Makun shekaru da dama a baya tun kafin zuwan Hajj Reporters.
“Na yi aiki da shugaban hukmar alhazan nan. Na san shi a mutum ma’aikaci kuma baya wasa da aiki. Saboda haka ya cancanta da wannan muƙamin da aka bashi. Shi ya sa ma muka zo mu taya shi murna a bisa nuƙamin da ya samu.
Haka kuma tawogar ta yabawa gwamnan Jihar Niger, Sani Bello abisa fikirar da yayi wajen naɗa wanda yake da gogewa da ƙwarewa kan harkokin Hajji.”
Shugaban ƙungiyar ya ƙara da cewa shugabancin hukumar alhazan ta Niger ta aiwatar da tsari da ya zama ɗaya daga cikin mafi kyau a aikin Hajjin 2019, wacce har saida IHR ta ba hukumar lambar girma a kan haka.
Ya ce”jajircewar ka, ƙwazo da ƙwarewar aikin ka ce ta sanya muka baka wannan lambar girma,”
“Mun yi farin ciki cewa mai girma gwamna ya gasgata zaben da Hajj Reporters tayi maka na bada lambar girma sakamakon muƙamin da ya baka na shugabancin hukumar alhazai. Saboda haka muna taya ka murna matuƙa”