Bai kamata gwamnati ta riƙa kashe kuɗaɗe don ɗaukar nauyin aikin Hajji ba- Sarkin Dutse

0
354

 Mai martaba Sarkin Dutse, Alhaji Muhammadu Nuhu Sanusi ya ce bai kamata gwamnati ta riƙa kashe kuɗaɗen domin ɗaukar nuyin aikin Hajji ba, inda ya yi kira da masu ruwa da tsaki a harkar Hajji da kuma alhazai da su ƙirƙiro wani tsari mai ma’ana.
Sarkin ya faɗi hakan ne lokacin da tawogar Hukumar Hajji ta Ƙasa, NAHCON, ta kai masa ziyara a Jihar Jigawa.
Sarkin ya kuma nuna farinciki da goyon baya kan sabon tsarin adashin gata da NAHCON ke shirin ƙaddamarwa.
Sarkin ya kuma tuna cewa an ɗauki tsawon shekaru NAHCON tana samun canje-canje masu kyau a harkar aikin Hajji .
Ya kuma nuna farin cikin sa cewa ziyarar itace irin ta ta farko da aka kawowa masarautar ta sa

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here