Shugaban Hukumar Alhazai ta Ƙasa, NAHCON, Alhaji Zikrullah Kunle Hassan ya jagoranci tawogar hukumar ta kai ziyarar aiki zuwa Jihar Katsina.
Mataimakin Gwamnan Jihar, Mannir Yakubu ne ya tarbi tawogar.
Ziyarar cigaba ne da ziyarar ayyukan cigaba da hukumar ke aiwatarwa a Jihar Katsina.
Da saukar sa a Jihar, Zikrullah Kunle ya ziyarci Hukumar Alhazai ta Jihar inda Direktan hukumar, Alhaji Suleman Nuhu Kuki ya tarbe shi, inda daga nan ya zarce da ziyarar ayyukan a Jihar