Bayan sun karɓe kuɗaɗen ajiyar su, maniyyata 43 sun sake dawo da su a Kano

0
391

 

 

Daga Jabiru Hassan da Mustapha Adamu, Kano

 

 

 

 

Hukumar kula da Jindaɗin Alhazai  ta 

Jihar Kano ta ce ta mayarwa maniyyata 380 kuɗaɗen su da suka ajiye domin zuwa aikin Hajjin 2020, wanda Mahukunta a Ƙasar Saudi Arebiya suka hana ƴan ƙasashen waje zuwa sakamakon annobar cutar corona.

 

A wata ganawa da mai rahoto daga Hajj Reporters Hausa ranar Litinin, Jami’ar Hulɗa da Jama’a ta hukumar, Hajiya Hadiza Abbas Sanusi ta bayyana cewa daga cikin maniyyata 380 ɗin da suka karɓe kuɗaɗen nasu, 43 sun dawo da shi da niyyar zuwa aikin Hajjin 2021.

 

“Daga bisani kuma sai ga maniyyata 43 sun sake maido mana da kuɗaɗen da suka karɓa da kansu. Wataƙila bayan shawarar da suka yanke na su maido kuɗaɗen ne domin su jira zuwa Hajjin shekara mai zuwa,” in ji ta.

 

Hajiya Hadiza ta sanar da cewa a bana, jimullar maniyyata 1794 ne suka yi ajjiyar kuɗaɗen su domin aikin Hajjin 2020, amma daga bisani 380 suka karɓe kuɗaɗen su kafin 43 su dawo da shi.

 

Ta kuma bayyana ce a halin yanzu kuɗaɗen maniyyata 1,457 ne su ka bar kuɗaɗen su domin zuwa Hajjin 2021.

 

 Ta yabawa yadda maniyyatan Jihar Kano suke fahimtar dukkanin tsare-tsaren da hukumar kula da jin daɗin alhazan ke yi duk shekara.

 

Hajiya Hadiza Abbas Sanusi ta kuma sanar da cewa ƙofar hukumar a buɗe take domin bada sahihan bayanai kuma masu gamsar wa ga maniyyata, musamman ganin cewa hukumar tana aiki ne domin tabbatar da cewa al’amura suna tafiya cikin nasara.

 

A ƙarshe, jami’ar ta yabawa babban sakataren hukumar, Alhaji Mohammad Abba Ɗambatta bisa yadda yake jagorancin hukumar cikin nasara, tare da godewa daukacin ma’aikata da jami’an alhazai na yankunan ƙananan hukumomi 44 dake jihar ta Kano saboda ƙoƙarin da suka yi wajen ganin hukumar ta kasance abar misali a ko da yaushe

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here