Daga Mustapha Adamu
Shugaban Hukumar Hajji ta Ƙasa (NAHCON), Alhaji Zikrullah Kunle Hassan ya suffanta Jihar Kano a matsayin jigo a jigilar aikin Hajji a Nijeriya.
Alhaji Hassan ya bayyana haka ne lokacin da ya kaiwa gwamnan Kano, Abdullahi Umar Gabduje ziyara a masaukin Jihar Kano, Asokoro, Abuja ranar Litinin.
Shugaban ya tabbatarwa da gwamnan ƙudirin hukumar na yin aiki kafaɗa da kafaɗa domin bunƙasa walwalar alhazan jihar, inda ya ƙara da cewa”Kano na da matuƙar muhimmanci wajen harkokin Hajji a Nijeriya,”
Da yake nasa jawabin, Gwamna Gabduje ya ce Kano gida ce ga Hukumar Hajji ta Ƙasa, “saboda tarihi ma ya nuna cewa Kano ce ƙashin bayan hukumar Hajji a Nijeriya.”
Ya tunawa tawogar cewa mutanen Kano na cikin na farko-farko da suka je aikin Hajji zuwa Saudi Arebiya a kan doki.
Ya kuma jaddada cewa gwamnatin Kano za ta yi aiki kafaɗa da kafaɗa da hukumar a ko da yaushe.
“Abin takaici, ba samu damar yin aikin hajji a bana ba sakamakon annobar corona. Waɗanda suka nemi a basu kuɗin su an basu.
“Suma waɗanda suka zaɓi su cigaba da ajiye kuɗaɗen su da hukumar saboda aikin Hajjin baɗi ana nan ana kular musu da dukiyoyin su,” in ji Ganduje