Mahjjata 25 na 2019 sun maka kamfanin sufurin jirgin sama a kotu

0
198

 

 

 

Adadin alhazai 25 ne ƴan ƙasar Malaysia suka kai ƙarar wani kamfanin sufurin jirgin sama ƙara a kotu, bayan da suke zargin sa da cutar su kuɗin ƙasar RM634,000 a Hajjin 2019.

 

Mahajjatan, waɗanda suka kasance a halin ba su ga tsuntsu basu ga tarko a filin tashi da saukar jiragen sama na King Abdul’aziz da ke Jidda a ranar 5 ga watan Agusta, sun maka kamfanin a kotu, inda suke ƙoarafin cewa bai biya su cikakkun kuɗaɗen da suka biya ba.

 

Ɗaya daga cikin mahajjatan, Muhammad Radhi Shariff Hussain, ɗan shekara 56 ya yi ƙorafin cewa sun bawa kamfanin isasshen lokaci na ya dawo musu da kuɗaɗen su amma bai dawo da su duka ba sai ƴan kaɗan.

 

“hakan ya jefa mu a halin ƙunci saboda da yawan mu ba masu arziƙi bane” ya faɗawa manema labarai a wata ganawa da yayi da su tare da waɗanda abin ya shafa su 14 daga cikin 25 ɗin tare da lauyoyin su a yau.

 

Ya kuma bayyana cewa a ranar da matsalar ta faru, tun da wuri kamfanin bai faɗa musu cewa ba wani wakili da zai raka su zuwa lokacin da za su tashi ba a Jidda.

 

“Bayan mun sauka a filin tashi da saukar jiragen sama na Jidda, Jami’an kula da shige da ficen ƙasar basu bar mu mun shige ba saboda bayan an duba bizar mu sai aka ga ashe ba sahihiya bace. Daga nan sai muka kai rahoto ga ƴan sanda.”

 

An gano cewa an biya mahajjatan RM30,000 zuwa 50,000 domin su yi bizar zuwa aikin Hajji mai suna furada, wacce ake yin ta kai tsaye daga ofishin jakadancin Saudi Arebiy

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here