Kaduna tafi kowacce jiha amfana da ayyukan mu- NAHCON

0
228

 

 

Hukumar Hajji ta Ƙasa (NAHCON) ta bayyana cewa Jihar Kaduna tafi kowacce jiha amfana da ayyukan hukumar a duk jihohin ƙasar nan.

 

Shugaban hukumar, Barista Zikrullah Kunle Hassan ne ya bayyana hakan lokacin da ya jagoranci tawogar hukumar ta kaiwa Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir Ahmad El-Rufai ziyara a gidan gwamnati ranar Laraba.

 

Ya lissafa irin ayyukan, waɗanda suka haɗa da ginin otal ɗin alhazai da yake gudana a halin yanzu, babban ɗakin taro, adashin gata na zuwa aikin Hajji da kuma cibiyar horaswa kan makamar aikin Hajji.

 

Alhaji Zikrullah ya kuma buƙaci gwamnatin jihar da ta samar da ofishin tuntuɓa na hukumar a jihar domin sauƙaƙa harkokin aikin Hajji a jihar wacce take ɗaya daga cikin jihohin dake da yawan alhazai.

 

A nashi jawabin, sakataren gwamnatin jihar, Balarabe Abbas Lawan, wanda ya wakilci gwamnan, ya bayyana cewa gwamnatin na shirin buɗe wata ma’aikatar ta harkokin aikin Hajji domin bunƙasa walwalar mahajjatan jihar.

 

Ya kuma tabbatarwa NAHCON cewa gwamnatin jihar za ta haɗa kai da ita domin sauƙaƙa harkokin aikin Hajji a jihar.

 

Haka kuma tawogar ta NAHCON ta kaiwa Sarkin Zariya, Dakta Shehu Idris ziyara a fadar sa domin neman goyon bayan masarautar kan hada-hadar aikin Hajji cikin nasara a jihar.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here