Daga Mustapha Adamu
Hukumar Hajji ta Ƙasa, NAHCON da bankin Ja’iz sun ƙulla yarjejeniya da kuma ƙaddamar da adashin gata na zuwa aikin Hajji.
An yi taron ƙaddamarwar ne a babban ɗakin taro na hukumar a ranar Alhamis.
A jawabin buɗe taron, Shugaban NAHCON ɗin, Alhaji Zikrullah Kunle Hassan ya ce ” adashin gata na zuwa aikin Hajji wani tsari ne da ke ƙunshe a dokar samar da NAHCON ta 2006 a matsayin wani shiri na tara kuɗin zuwa aikin Hajji ga maniyyatan dake don zuwa Hajji a ƙasa mai tsarki.”
Shugaban ya yabawa shugabannin baya na NAHCON, da suka haɗa da Mallam Muhammad Musa Bello da kuma Barista Abdullahi Muhammad Mukhtar a bisa jajircewa da hangen nesa da suka yi wajen ƙirkíro da dokar.
”dole na yabawa shugabannin baya saboda sun jajirce wajen samar da tsarin adashin gatan nan inda suka yi bulaguro zuwa Malaysia da Indonesiya domin ƙaro sani da kuma ganawa da masana a kan shirin,”
”a yau muna ƙaddamar da tsarin da a ka kwashe tsawon shekaru 10 ana ƙoƙarin samar da shi, wanda ya ma riga hukumar Hajji ta ƙasa samuwa. Haka kuma haɗin gwiwar da aka yi da banki an yi ne domin a gaggauta ƙaddamar da tsarin.
”abinda nake nufi a nan shine wannan taron na yau ana yin shi ne domin mu samu lasisi daga Babban Bankin Ƙasa, CBN domin aiwatar da tsarin cikakken.”
A nashi ɓangaren, Babban Manajan Ja’iz ɗin, yabawa ƙwazon shugabancin hukumar na da da na yanzu yayi wajen tabbatuwar tsarin.
Ya kuma godewa shugabancin bankin abisa taimakawa wajen tabbatar da tsarin na adashin gata, inda ya ce ” ba ma wai don ya dace a haɗa kai da banki ba, sai dan ma ya zama cewa wata buƙata ce da al’ummar ƙasa suke kira da a yi kuma gashi ya tabbata.”
Shima babban shugaban Ja’iz ɗin, Umar Mutallib ya ƙara da cewa rattaba hannu a yarjejeniyar wata babbar nasara ce ga duk masu ruwa da tsaki a harkar Hajji.
Ya bayyana cewa tsarin zai bawa al’ummar Musulmi damar tara kuɗi domin cika burin su na sauke farali.