Saudiya za ta buɗe jigilar jiragen sama na ƙasashe ran 15 ga Satumba

0
430

 

 

A ranar Asabar, 15 ga watan Satumba Saudi Arebiya za ta ɗage dakatarwar da ta yi a jigilar jiragen sama.

 

Amma kuma ba duka aka ɗage dakatarwar ba, sai dai wasu zaɓaɓɓun rukunin al’umma kamar haka:

 

Za a buɗe jigilar jiragen sama ga ƴan ƙasa, da suka haɗa da sojoji, ma’aikatan gwamnati, sai kuma farar hula waɗanda aka tura su wani aiki a waje.

 

Za buɗe jigilar jiragen sama ga ƴan ƙasashen waje da za su shigo sannan su fita daga ƙasar Saudiyya, amma sai idan suna da shaidar umarnin shiga ko fita daga ƙasar wato biza, shaidar umarni ta aiki da kuma shaidar umarni ta ziyara.

 

Sannan an yarjewa ƴan ƙasashen ɓangaren GCC su shiga Saudiyya.

 

Sharuɗɗan shiga Saudiyya ɗin sun haɗa da gwajin cutar corona wanda bai wuce awanni 48 ba.

 

Haka kuma Ma’aikatar Harkokin Waje ta Saudiyya ta bayyana cewa a watan Disamba mai zuwa ne ƙasar za ta yi gyara na ƙarshe kan dakatarwar, inda ta ƙara da cewa za ta ci gaba da canja matakan da ta ɗauka tare da haɗin kai da aiwatarwa daga Hukumar Lafiya ta ƙasar

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here