Sansanin Alhazai: IHR tayi kira ga gwamnonin Naija Delta da su kwaikwayi Obaseki

0
6

Daga Mustapha Adamu

Independent Hajj Reporters, Ƙungiya mai zaman kan ta da ta ke kwai rahotanni kan Hajji da Ummara ta yabawa Gwamnan Jihar Edo, Godwin Obaseki a kan gina sansanin Alhazai a jihar.

Wannan na ƙunshe a wata sanarwa da ƙungiyar ta fitar ranar Talata, mai ɗauke da sa hannu na haɗin gwiwa tsakanin Shugaban ta na Ƙasa, Ibrahim Muhammad da Sakataren Yaɗa Labaran ta, Abubakar Mahmoud.

”Muna yabawa mai girma Gwamnan Jihar Edo, Godwin Obaseki sakamakon gina sabon sansanin Alhazai domin al’ummar musulmai a jihar,” in ji IHR.

Sanarwar ta ƙara da cewa ”IHR ta lura da kuma yabawa da ƙoƙarin Shugaban Hukumar Hajji ta Jihar Edo sakamakon gina wata gada ta haɗin kai tsakanin al’ummar jihar, da kuma jajircewar Obaseki ta ganin cewa an kammala aikin.

IHR ta kuma yi jan hankali ga sauran gwamnonin jihohin yankin kudu maso kudu da su riƙa bawa harkar addinai daban-daban muhimmanci, inda ta ce hakan zai kawo haɗin kai tsakanin al’umma kamar yadda Obaseki yayi.

”A matsayin mu na kungiya da ta maida hankali a kan Hajji da Ummara a ƙasa, zamu ci gaba da ƙarfafa gwiwa da goyon bayan duk wasu ɗaiɗaikun mutane da kungiyoyi da ma’aikatun gwamnati da suke samar da ayyuka da gine-ginen da zasu kawo cigaba da Walwalar alhazai a ƙasar nan,” sanarwar tace 

Bayan mun yabawa Obaseki, muna kira ga sauran gwamnoni da su gina sansanin alhazai da ofisoshin harkar Hajji na dindindin a jahohin su domin bunƙasa walwalar alhazai.

IHR ta tuna cewa kafin ƙaddamar da sansanin alhazan, ta rubutawa Gwamna Obaseki takardar yabo a bisa gina sansanin da kuma samar da taimako da kulawa ga alhazan Jihar Edo a lokacin aikin Hajjin 2019

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here