Hajj Reporters jigo ce a harkokin aikin Hajji a Nijeriya- Shugaban Hukumar Hajji ta Abuja

0
280

 

 

Babban Daraktan Hukumar Hajji ta Abuja, Mallam Nasiru Ɗanmallam ya suffanta Independent Hajj Reporters, IHR,  da cewa ƙungiyar ƙashin bayan harkokin aikin Hajji ce a Nijeriya.

 

Daraktan ya kuma tabbatar da aniyar sa ta haɗin gwiwa da IHR ɗin wajen bawa ma’aikatan hukumar horo.

 

Mallam Nasiru ya bayyana hakan ne lokacin da shugabannin ƙungiyar suka kai masa ziyara ta musamman a ofishin sa, a bisa jagorancin shugaban ta na ƙasa, Mallam Ibrahim Muhammad ranar Alhamis.

 

Ya siffanta IHR a matsayin jigo a harkokin Hajji da Ummara a ƙasar nan.

 

”tun zuwa nan, Independent Hajj Reporters ce ƙadai ƙungiya mai zaman kanta da ta yi shura wajen zama ƙashin bayan harkar Hajji da Ummara wacce na yi mu’amala da ita.

 

”A guri na, ku kuke jagorancin kawo rahotannin harkokin aikin Hajji a Nijeriya, saboda a gani na, ku kaɗai na sani. 

 

”zan ɗora daga inda shugabannin baya suka tsaya a kan tsohuwar alaƙar hukumar nan da ƙungiyar ku”

 

A nashi jawabin, Mallam Muhammad ya jaddada ƙudurin ƙungiyar wajen haɗa gwiwa da hukumar da masu ruwa da tsaki a kan ƙarawa mahajjata ilimi da wayar da kai.

 

Ya ƙara da cewa yanzu Hajji ya bambanta da kafin ɓullar annobar COVID-19.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here