Daga Mustapha Adamu
Hukumar Hajji ta Ƙasa, NAHCON, ta bayyana cewa Marigayi Sarkin Zazzau, Alhaji Dakta Shehu Idris ya rasu ne a lokacin da ake matuƙar buƙatar irin su wajen cimma ƙudurin gwamnatocin tarayya da na Jihohi na kawo haɗin kai a Nijeriya.
A wata sanarwa da Jami’ar Hulɗa da Jama’a ta NAHCON, Fatima Sanda Usara ta fitar a ranar Litinin, Hukumar ta bayyana alhinin ta na rasuwar Mai Martaba Sarkin Zazzau ɗin.
Sanarwar tace a madadin Shugaban hukumar, Barista Zikrullah Kunle Hassan, a madadin manyan jami’ai da ma’aikatan ta, NAHCON na jimamin rasuwar Sarkin wanda yake mutum ne na mutane.
”NAHCON na miƙa ta’aziyar ta ga Shugaban Ƙasa , Muhammadu Buhari da Gwamna Nasir El-Rufai na Kaduna, iyalan mamacin da kuma ɗaukacin al’ummar Jihar Kaduna a bisa babban rashin da aka yi.
”Muna addu’ar Allah Yai masa rahma, Ya sa aljannar firdausi ce makomar sa. Allah Ya bawa iyalin sa juriyar rashin sa,” in ji sanarwar