Bayan zargin wawure N38m, tsohon Shugaban Ƙaramar Hukuma ya samu muƙami a Hukumar Hajji ta Yobe

0
436

 

Gwamnan Jihar Yobe, Mai Mala Buni ya amince da naɗin tsohon Shugaban Ƙaramar Hukumar Potiskum, Mohammed Musa Potiskum, a matsayin Shugaban Gudanar da Ayyuka na Hukumar Hajji ta Yobe.
Tun a baya ne dai Hajji Reporters ta wallafa labarin dakatar da Mohammed Potiskum a matsayin Shugaban Ƙaramar Hukuma da tsohon Gwamnan Jihar, Ibrahim Geidam yayi, sakamakon zargin karkatar da akalar N38 miliyan na kuɗaɗen alhazan Jihar na 2017 su 33.
Amma abin mamaki, sai gashi tsohon Shugaban Ƙaramar Hukumar ya samu muƙami a Shugaban Gudanar da Ayyuka na Hukumar Hajji ta Yobe.
Ba ma wai ya shiga jerin ƴan takarar neman muƙamin ba, Mohammed Potiskum ya samu muƙamin a Hukumar da ake zargin ya aikata wannan badaƙala.
Sabon muƙamin na Mohammed Potiskum ya yamutsa hazoa jihar ta Yobe, inda masu sharhi suke ganin hakan zai sanya al’umma, musamman maniyyata aikin Hajji su yanke ƙauna da gwamnatin.
Hakan ne ya sanya suke kira ga gwamna Buni da ya yi duba na tsanaki a kan muƙamin, in ya so ya canja masa da wani muƙamin a wata ma’aikatar.
A tuna cewa a wata sanarwa da kakakin Sakataren Gwamnatin Jihar, Shuaibu Abdullahi ya fitar a 2017, tsohon gwamnan jihar, Geidam ne ya dakatar da tsohon shugaban ƙaramar hukumar abisa bayanan da kwamitin binciken da Majalisar Jihar ta kafa, inda ta gano cewa Mohammed Potiskum da sauran ma’aikatan sa sun wawure kuɗaɗen

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here