Za a dawo da yin Ibadar Ummara daga 4 ga Oktoba

0
315

 

Ma’aikatar Harkokin Cikin Gida ta Saudi Arebiya ta sanar da cewa za ta bada damar a cigaba da Ibadar Ummara, Amma daki-daki daga ranar 4 ga watan Oktoba, daidai da 21 ga watan Safar, 1442 AH.

 

Ma’aikatar ta ce kashi na farko da za su fara aikin Ummaran sune ƴan ƙasa da kuma mazauna ƙasar inda za su yi Ibadar a cikin ƙasar daga ranar Lahadi, 17 ga watan Safar, 1442 AH, inda kashi 30 cikin 100 ne, wato mutane 6000 aka yarda su yi Ibadar a rana a wani mataki na kariya a babban masallaci mai tsarki.

 

Mataki na biyu kuma zai bawa ƴan ƙasa da mazauna ƙasar 15,000 damar yin Ummara, ziyara da Sallah daga ranar Lahadi, 1 ga watan Rabi’ul Auwal 1442 AH, a matakin kashi 75 cikin 100 a rana. 

 

Sannan masallata 40,000 a rana za su yi sallah a babban masallacin amma a cikin matakai na tsafta da kariya daga ɗaukar cututtuka.

 

 

Mataki na uku kuma zai bawa ƴan ƙasa da baƙi daga wasu ƙasashe damar yin Ummara da sauran ibadu daga ranar 15 ga watan Rabi’ul Auwal.

 

Ma’aikatar tace mutane 20,000 ne za su riƙa yin Ummara, sannan 60,000 su yi salloli a babban masallaci a rana ga ƴan ƙasa da baƙi har sai ranar da corona ts tafi, to shine za a dawo yin Ummara a kashi 100 kamar yadda a ka saba a baya.

 

Mahajjatan Ummaran sai sun nuna shaidar sahalewar yin Ummara ɗin bayan sun nemi sahalewar wa ce za a fara aika neman a ranar 10 ga watan Safar kuma wanda zai yi ummar ya tabbata bashi da corona.

 

Ma’aikatar Hajji da Ummara za ta samar da tsare-tsaren jigilar masu Ibadar Ummara ɗin ta zuwa da komawa daga babban masallaci.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here