NAHCON za ta horas da ma’aikatan hukumomin alhazai na jihohi kan Adashin Gata na Hajji

0
8

Daga Mustapha Adamu

Hukumar Hajji ta Ƙasa, NAHCON ta bayyana cewa za ta bawa jami’an hukumomin kula da jin daɗi da walwalar alhazai na jihohi horo a kan sabon tsarin nan mai suna Adashin Gata na Aikin Hajji.

Horon zai taimaka wajen ƙara musu sani a kan tsarin, a matsayin su na masu ruwa da tsaki a harkar Hajji a Nijeriya, kamar yadda sanarwa mai ɗauke da sa hannun Jami’ar Hulɗa da Jama’a ta NAHCON ɗin, Fatima Sanda Usara ta fitar a ranar Alhamis.

Shugaban NAHCON ɗin, Barista Zikrullah Kunle Hassan ne ya bayyana hakan yayin da ya kai ziyarar duba ayyukan cigaban Hajji a Jihar Adamawa.

Barista Zikrullah ya yaba kan yadda aikin ya ke tafiya, inda ya kai matakin kashi 70 cikin 100, kamar yadda wakili daga Ma’aikatar Ayyuka to Adamawa dake Yola.

Akwai masauki mai kama da otal da yake ɗauke da ɗakuna 64, sai kuma masallacin sansanin alhazai na jihar da aikin sa ya kammala 100 bisa 100, yayin da ake ci gaba da aikin gina babban ɗakin taro da kuma banɗakuna.

Duk da cewa Shugaban NAHCON ɗin ya nuna rashin gamsuwa da saurin aikin, amma ya yabawa ɗan kwangilar, inda ya bashi wa’adin watanni biyu da ya kammala aikin. 

Bayan haka kuma tawogar NAHCON ɗin ta kai ziyara ta musamman ga Gwamnan Jihar Adamawa, Ummaru Fintiri da kuma kuma wasu jami’an Hukumar Kula da Walwalar Alhazai ta jihar.

A nan ne ma shugaban NAHCON ɗin yai amfani da wannan damar ya faɗakar da jami’an hukumar kan tsarin nan na Adashin Gata na Aikin Hajji da kuma Samar da Cibiyar Horaswa kan Aikin Hajji, Maida Tsare-tsaren Aikin Hajji zuwa Yanar Gizo da kuma Rage yawan kwanakin da alhazai suke yi a Saudiyya.

A gidan gwamnati kuma, Barista Zikrullah ya roƙi gwamnatin jihar da ta kawowa NAHCON ɗauki wajen gina kwatoci a sansanin alhazai, samar da tituna zuwa sansanin da kuma sasantawa tsakanin waɗanda suka cinye filaye mallakar NAHCON ɗin.

A nashi jawabin, gwamnan jihar, wanda Shugaban Ma’aikatan Gidan Gwamnati, Farfesa Giɗaɗo ya wakilta, ya jaddada ƙudurin gwamnatin na taimakawa NAHCON a kowanne lokaci.

A nashi ɓangaren, Shugaban Hukumar Alhazai ta Jihar, Dakta Salihu Abubakar ya bayyana farin cikin sa a kan tsare-tsaren da hukumar take bijiro da su, in da ya nemi cewa jami’an hukumar sa za fara horaswa a kan tsare-tsaren.

Ya kuma bayyana cewa maniyyata 52 ne kacal suka karɓe kuɗaɗen su bayan an soke Hajjin 2020, inda ya ce tuni a ka kammala biyan su kuɗaɗen

 

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here