Awanni uku kawai za a riƙa yi a Ummara

0
554

Yayin da Saudi Arebiya ke shirin buɗe aikin Ummara a ranar 4 ga watan Oktoba, awanni uku kawai aka bawa kowa yayi Ummara a matakin farko idan aka dawo da yin ibadar.

Kowanne mai yin Ummara zai yi ta ne a iya guraren da ake yin Ummara na birnin Makka kaɗai.

Jaridar Arab News ta rawaito cewa za a yi ummarar ne ta amfani da wata manhajar wayar salula mai suna I’tamarna.

An yi tsarin ne domin amfani da guraren yin aikin ummarar na birnin mai tsarki, inda mutane 6,000 ne kaɗai za su riƙa yin ibadar a rana ɗaya, a lokuta 6 daban-daban kuma a rukunin mutane dubu ɗaya-ɗaya waɗanda za su yi awanni uku sai su bawa wani rukunin dama suma su zo su yi tasu ummarar.

Ahmed Bajaiffer, wanda yake da hannayen jari a kamfanonin da ke harkar ummara ya bayyana cewa Gwamnatin Saudiyya ta ɗauki matakin dawo da Ummarar ne bayan an dakatar da ita sakamakon annobar corona ganin dacewar cigaba da ibadar amma ta hanyar kiyayewa da matakan kariya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here