COVID-19: Kano da IHR za su haɗa gwiwa don horaswa kan sabbin tsare-tsaren Hajji da Ummara

0
464

 

 

Daga Mustapha Adamu da Jabiru Hassan

 

 

Gwamnatin Kano da Ƙungiyar Ƴan Jarida masu Kawo Rahotanni kan Hajji da Ummara mai Zaman Kanta, wacce aka fi sani da Independent Hajj Reporters (IHR) za su haɗa gwiwa wajen horaswa a kan sabbin tsare-tsare kan Hajji da Ummara da a ka ɓullo da su sakamakon annobar cutar COVID-19.

 

Horaswar dai za a yi ta ne ga ma’aikatan  Hukumar Jin Daɗi da Walwalar Alhazai ta jihar domin su horu da sabbin tsare-tsare da Saudi Arebiya ta ɓullo da su sakamakon annobar cutar corona.

 

Kwamishinan yaɗa labarai na jihar, Mallam Muhammad Garba ne ya tabbatar da hakan yayin da ya karɓi tawogar IHR da ta kai masa ziyara a ofishin sa ranar Talata, a bisa jagorancin shugaban ta na ƙasa, Alhaji Ibrahim Muhammad.

 

Kwamishinan, duba da irin matsalolin da annobar corona ta haifar a harkoki da dama a faɗin duniya, ya bayyana muhimmancin haɗin gwiwar wajen horas da ma’aikatan hukumar alhazan domin su fahimci sabbin shirye-shirye da Saudiyya ta ɓullo da su don tunkarar aikin Hajjin 2021.

 

Tsohon Shugaban Ƙungiyar Ƴan Jarida na Ƙasa (NUJ) ya yi bayani kan muhimmancin kafafen yaɗa labarai wajen wayar da kai da ilimantarwa ga maniyyata, inda ya jaddada haɗin gwiwar gwamnatin jihar da IHR wajen cimma wannan buri.

 

“Haɗin gwiwar nan na da matuƙar muhimmanci duba da cewa abubuwa na canjawa da kuma yadda cutar corona ta kawo canji na tsare-tsare wanda zai bambanta da na baya idan Hajjin 2021 ya zo.

 

“Saboda haka kafafen yaɗa labarai na da matuƙar muhimmanci wajen ilimantarwa da wayar da kai kuma ƙungiyar IHR ta daɗe tana taka rawar gani a wannan ɓangare.

 

“Tabbas kafafen yaɗa labarai na da gagarumar rawa da za su taka wajen wayar da da maniyyata kai a kan sabbin tsare-tsare da Saudiya ta ɓullo da su. Saboda haka wannan haɗin gwiwa da ku ta zama dole domin mahajjatan mu su bi ƙa’idoji su kuma yi aikin hajji cikakke a haɗin,”

 

Tun da farko, Shugaban IHR na Ƙasa, Alhaji Ibrahim Muhammad ya bayyana cewa corona ta canja tsare-tsaren aikin Hajji da Ummara a duniya, inda ya ƙara da cewa yana da kyau ma’aikatan hukumar alhazan Kano su samu horo kan sabon tsarin da a ka samu duba da muhimmancin Kano a aikin Hajji.

 

Ya ce sabbin tsare-tsaren da Hukumomin Saudiyya suka ɓullo da su sun sha bambam da waɗanda aka sani aka kuma saba da su sakamakon ɓullar annobar corona wacce ta lalata kowanne ɓangare na rayuwa.

 

Shugaban IHR ɗin ya bayyana cewa ƙungiyar ta rattaba hannu a yarjejeniya da jaridu na ƙasashen waje, har da Saudiyya domin ƙara faɗaɗa samun bayanai da wayar da kai kan Hajji da Ummara.

 

Tun da farko dai ƙungiyar ta kaiwa Shugaban Hukumar Jin Daɗi da Walwalar Alhazai ta Kano, Abba Mohammed Ɗambatta, wanda ya yabawa IHR a kan irin ƙoƙarin da take yi na ilimantarwa da wayarwa Alhazai da maniyyata kai a kan Hajji da Ummara.

 

Ya kuma ci alwashin haɗin gwiwa da ƙungiyar domin horas da ma’aikatan hukumar a kan sabbin tsare-tsaren da Saudiyya ta ɓullo da su sakamakon annobar corona.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here