Shugaban Hukumar Hajji ta Ƙasa, (NAHCON)Barista Zikrullah Kunle Hassan ya bayyana cewa a garin Maiduguri na Jihar Borno jirgin farko na alhazai na Hajjin 2021 zai fara tashi.
Ya ce matakin fara jigilar alhazai a Maidugurin ya zo ne sakamakon roƙon da Mataimakin Gwamnan Jihar Borno ya miƙa ga NAHCON lokacin da tawogar hukumar suka kaiwa Gwamnan jihar, Babagana Umara Zulum ziyara.
Ƙarin bayani na nan tafe…