Ba za a bar wanda ake zargi da corona ya shiga Masallacin Harami ba

0
298

 

Duk wanda ake zargin yana ɗauke da ƙwayar cutar corona ba za a bar shi ya shiga Masallacin Harami ba a ranar da za a dawo aikin Ummara na mataki-mataki ranar 4 ga watan Oktoba, inji Ofishin Shugabancin kula da harkokin Masallatan Harami Biyu.

Ahmed Al-Mansouri, Mataimakin Shugaban Ofishin Shugabancin kula da harkokin Masallatan Harami Biyu ne ya faɗi hakan yayin da yake ganawa da manema labarai a kan shirye-shirye na buɗe aikin Ummara da ziyarci -yace zuwa masallaci mai tsarki.

Ya ƙara da cewa Hukumar Lafiya ta Ƙasar Saudi Arebiya ta samar da cibiyoyin kula da marasa lafiya masu ɗauke da cikakkun kayan aiki domin duba waɗanda suka kamu da corona a yayin aikin Ummara.

Al-Mansouri ya yi bayanin cewa za a riƙa yiwa rukunonin masu aikin Ummarar jagora zuwa wajen ɗawafi, inda ya ƙara da cewa za a ajiye jagorori 16 a filin Ka’aba ɗin domin nunawa mutane guraren da za su je a cikin Masallacin Harami.

Ya kuma bayyana cewa za a maƙala na’urorin ɗaukar hoto masu busa iska mai ɗumi a masallacin Harami ɗin, inda ya ƙara da cewa an hana zaman ittikafi da kuma shigowa da abinci.

Ya ce za a riƙa wankewa da feshin magani a dukka banɗakunan cikin Masallaci mai Tsarkin sau 6 a rana.

Sannan, in jishi, za a riƙa feshin magani a jikin shimfiɗu, kujerun guragu da kuma benaye masu amfani da na’ura.

Ya kuma ce a kowacce rana za a riƙa amfani da wani haske wajen goge na’urorin sanyaya waje da na fitar da iska sau da yawa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here