NAHCON ta ƙaddamar da shirin Adashin Gata na Hajji a Kano

0
10

Daga Jabiru Hassan, da Mustapha Adamu, Kano

Hukumar Hajji ta Ƙasa, NAHCON ta ƙaddamar da shirin Adashin Gata na Aikin Hajji a hukumance a Jihar Kano.

NAHCON ta ƙirƙiro da shirin ne domin bawa musulman Nijeriya, masu kuɗi da marasa ƙarfi damar zuwa aikin Hajji a ƙalla sau ɗaya a rayuwa.

Da yake yin bayani a yayin taron, wanda a ka yi a Sansanin Alhazai a Kano ranar Lahadi, Shugaban NAHCON, Barista Zikrullah Kunle Hassan ya bayyana farincikin sa da tabbatuwar shirin.

A cewarsa, NAHCON ta kwashe sama da shekaru 10 tana shirin ƙirƙiro tsarin adashin gatan kamar yadda sashe na 7 (1) na dokar da ya kafa hukumar ya bada umarni.

Ya ƙara da cewa shirin adashin gatan da NAHCON ta ƙaddamar shine irin sa na farko a nahiyar Afirka.

Hassan yayi bayanin cewa sun haɗa gwiwa da bankin Ja’iz ne duba da cewa baya ta’mmali da kuɗin ruwa kuma yana da riƙon amana.

Ya kuma bayyana cewa shirin zai tallafawa marasa ƙarfi su yi tarin kuɗi , inda ya ƙara da cewa zai taimaka wajen bunƙasa tattalin arziƙin al’umma.

Shugaban ya taya hukumar, shugabanni  da kuma ma’aikatan ta a bisa ƙoƙarin su na tabbatar da shirin da kuma sauran abubuwan cigaba da ta samu tun zuwan shugabancin su.

A nashi ɓangaren, Gwamnan Jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje ya shwarci al’umar jihar da su shiga cikin shirin domin tara kuɗin zuwa aikin Hajji cikin sauƙi.

“Wannan shirin yazo daidai da zamani kuma akwai bukatar ganin cewa mutane sun shiga shirin ta yadda kowa zai iya samun damar sauke farali cikin sauki duba da halin da ake cikin na tattalin arziki a duniya baki data.

Gwamnan ya yabawa NAHCON da bankin Jaiz saboda ƙoƙarin da suka yi wajen ƙirkíro da shirin domin taimakawa Al’umar musulmi su sami damar sauke faralin su ta hanyar ajjiye kuɗaɗe.

Ganduje ya kuma bawa ma’aikatan gwamnatin jihar da su shiga shirin domin su samu damar zuwa Hajji a rayuwar su.

A nasa tsokacin, Sarkin Musulmi,  Muhammad Sa’ad ko, wanda Sarkin Bichi, Nasiru Ado Bayero ya wakilta, yayi fatan alheri ga NAHCON da kuma bankin Jaiz saboda ɓullo da wannan shirin mai matuƙar amfani. 

Sarkin ya yi kira ga al’umar musulmi da su shiga cikin shirin mai albarka domin samun ikon tafiya aikin Hajji duk shekara.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here