DA ƊUMI-ƊUMI: Tsohon Kwamishina a NAHCON, Idoko ya rasu

0
424

 

Tsohon Kwamishina kuma mamba a Kwamitin Gudanarwa na Hukumar Hajji ta Ƙasa, NAHCON, Dafta Adam Idoko ya rasu.

Ya rasu a asibiti a Abuja bayan ya sha fama da jiyya.

Marigayi Idoko, wanda ya fito daga yankin ƙabilar ibo, mahaifi ne ga Barista Fauziyya ta sashin shari’a na NAHCON.

Tuni dai a ka binne marigayin a maƙabartar Gudu da ke Abuja, a bisa koyarwar addinin Musulunci.

Ƙarin bayani na nan tafe…

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here