Hukumar lafiyar Saudiyya ta shawarci wasu rukunnan marasa lafiya da su dakata da yin Ummara

0
935
UMRAH H

Hukumar lafiya ta Saudi Arebiya ta yi kira ga wasu rukunnan marasa lafiya da su ɗage yin Ummara da ziyara zuwa masallaci mai tsarki.

A wani jadawalin faɗakarwa da ta wallafa a shafinta na kafar sadarwa ta twitter, wanda ta yiwa laƙabi da “Live Well”, ma’ana, kasance cikin ƙoshin lafiya, hukumar ta ce waɗanda suke fama da matsanancin ciwon siga mara kan gado, hawan jini, cutar jeji da sauransu, kuma an kwantar da su a asibiti a watanni 6 da suka gabata, su haƙura da yin Ummara.

Marasa lafiyar sun kuma haɗa da masu fama da ciwon zuciya, rashin isassun sinadaran kariyar jiki, cutar ƙirji mai tsanani kuma an kwantar da su a asibiti a bara, sannan kuma da mata masu juna biyu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here