An fitar da sharuɗɗan shiga, kabarin ma’aiki

0
377
PROPHET MOSUQE RWAD

Babban Ofishin Kula da Masallatan Harami Biyu ya fitar da sharuɗɗa guda tara na shiga Rawdah, wato kabarin Annabi SAW.

1) Dole a aika buƙatar zuwa ta manhajar EatMarna kawai.
2) Mutum ya zo da shimfiɗar sallar sa. 
3) Banda gaisawa da hannu.
4) A zo a lokacin da aka sanya.
5) A riƙa tsaftace hannuwa da sinadarai.
6) A sanya takunkumi a fuska.
7) A tabbatar da tazara da juna.
8) Ma’aikata da jami’an tsaro kawai aka yarda su riƙa yin salloli 5 na rana da ta Juma’a a cikin Rawdah da cikin Masallacin Annabi, sai kuma waɗanda suka kawo jana’izar ƴan’uwan su da suka rasu.
9) Za a ci gaba da rufe masallacin Annabi bayan sallar isha, sannan a buɗe a awa ɗaya kafin sallar asuba

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here