Kamfanoni 531 sun shirya tarbar alhazan ƙasashen waje a zango na uku na dawowar Ummara

0
14

Adadin kamfanoni 531 ne suka shirya tsaf domin tarbar alhazan Ummara a zango na uku na dawowar Ummara na daki-daki da kuma da cigaba da ziyara a masallatai biyu masu tsarki da za a fara ranar 1 ga watan Nuwamba.

Amma za a yi hakan ne ta hanyar biyayya ga matakan kare kai daga kamuwa da cutar coronavirus domin kare lafiyar alhazan da za su zo daga wasu ƙasashen na waje, kamar yadda Kamfanin Dillancin Labarai na Saudiya ya rawaito.

Hani Al-Omairi, mamba a cikin kwamitin Hajji da Ummara da kula da Masaukai a Makka, ya ce kamfanoni da za su yi hidimar Ummara ɗin sun shirya kwasa-kwasai na musamman domin horas da ma’aikatan su.

Al-Omairi ya bayyana cewa wakilan alhazan Ummara na ƙasashen waje 6,500 waɗanda za su yi haɗin gwiwa da kamfanoni 531 ɗin domin tsara yadda miliyoyin musulmai daga faɗin duniya za su aiwatar da ibadar.

Ya ƙara da cewa akwai kuma dandali da gurare har 32 da za a iya ajiyewa mai sha’awa domin wasu shirye-shirye don baƙin alhazan.

”akwai sama da otal-otal 1,200 da ɗakuna sama da 270,000 a Makka da kuma sama da ɗakunan 75,000 a Madina kuma akwai nagartattun mataki-mataki  na ɗakunan da suka dace da matsayi na duniya.

”muna da matasan ma’aikata maza da mata har 14,000 a wannan ɓangare. Ana sa ran jigilar Ummara za ta samar da Riyal ta Saudiya sama da  biliyan 10, inda kashi 70 daga cikin kuɗaɗen za a samu ne daga harkokin otal otal, sufuri da sauran harkokin samun kuɗi a wannan kakar ta Ummara da muke ciki,”

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here