![Greater Kahsmir](https://hajjreportershausa.com/wp-content/uploads/2020/10/Greater-Kahsmir.jpg)
Ma’aikatar Kula da Hajji da Ummara ta Saudi Arebiya ta bayyana cewa sama da mutane 125,000 ne suka yi Ummara a zango na farko bayan buɗewa, amma kawo yanzu, ba a samu ɓullar cutar corona ba.
” A ranar Asabar ɗin da ta gabata ne a ka kammala zango na farko na Ummara inda muka karɓi Alhazai 125,000. Zango na farko ya taƙaita ne a kan Ummara, banda zuwa yin Sallah,” Amr Al-Maddah, Jami’i a Ma’aikatar.
Ya ƙara da cewa sau miliyan biyu da rabi aka sauke manhajar nan ya Eatmarna ta aikin Ummara.
A wata hira da yayi da Al-Ekhbariya, Al-Maddaha ya ce masallata 40,000 da kuma alhazan Ummara 15,000 ne suka ziyarci masallacin Harami a zangon Ummara na biyu.