Daraktan Jami’an Tsaron Jama’a, Laftanal Janar Khalid Al-Harbi ya bada umarnin a ɗauki mata sojoji guda 99 domin su tsare Kabarin Ma’aiki, da aka fi sani da Rawdah.
Hakan ya zo ne a wani mataki na aiwatar da umarnin Ministan Harkokin Cikin Gida, Yarima Abdul Aziz Bin Saud Bin Naif.
Sabbin jami’an tsaron za su fara aiki ne na kula da cunkoson mata da za su riƙa zuwa ziyara Rawdah ɗin daga makon gobe.
Waɗannan matan sun samu ƙwarewa ne bayan sun samu horo a duka ɓangaren aikin gudanarwa a ofisoshi da kuma na fita waje filin daga.
Wannan ya zo ne a sakamakon ƙudurin Sarkin Madina, Yarima Faisal Bin Salman na samun ɓangaren mata a sojin ƙasar da za su riƙa kawo tsaro a tsakanin matan da za su riƙa kawo ziyara kabarin ma’aiki.
A ranar 18 ga watan Oktoba ne a ka sake buɗe Rawdah ɗin bayan an samu tsaiko na watanni bakwai sakamakon ɓarkewar annobar corona.