Majalisar manyan malaman Saudiyya sun yi Allah wadai da ɓatanci ga Annabi

0
10

 

Majalisar Manyan Malami ta Saudi Arebiya ranar Lahadi ta tabbatar da cewa ɓatanci ga Annabi Mai Tsira da Aminci, da sauran annabawa da manzanni ba zai taɓa yi musu illa ba, sai dai kawai ya yiwa masu ra’ayin wuce gona da iri amfani, waɗanda suke yaɗa kiraye-kirayen tsana ga al’umma.
A sanarwar da ta fitar, Majalisar ta yi kira ga al’umma a faɗin duniya, da suka haɗa da ƙungiyoyi da ɗaiɗaikun mutane da su yi tir da wannan cin mutuncin, domin basu da alaƙa da ƴancin faɗin ra’ayi ko wata wayewa, sai dai kawai ana yi ne domin yiwa masu ra’ayin wuce gona da iri aiki a sadaka.
Sanarwar ta ƙara da cewa Musulunci ya hana zargin kowanne annabi da yin ƙarya ko aikata wani abu na ba daidai ba, sannan ya hana zagin manya a musulunci.
Majalisar ta ƙara da cewa, kamata ya yi musulmai su riƙa yaɗa tarihin Annabi Mai Tsira da Aminci, gami da bada misalai a kan jinƙansa, gaskiya, haƙuri da kuma aiki domin jin kyautatawa al’umma

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here