Ma’aikatar Hajji da Ummara ta Saudiya za ta sanar da ƙasashen da za su yi Ummara

0
351

 

 

Ma’aikatar Harkokin Hajji da Ummara ta Ƙasar Saudi Arebiya ta ce za ta rubutawa da sanar da ƙasashen da su ka cancanta su yi Ummara, wacce za a fara ranar 1 ga watan Nuwamba.

 

Ma’aikatar ta ce, a haɗin gwiwa da Hukumar Lafiya da Ma’aikatar Kula da Harkokin Waje da sauran hukumomin da abinda ya shafa, na aiki domin tantance ƙasashen da alhazan Ummara za su zo da kuma adadin su a lokaci zuwa lokaci.

 

Wannan zai faru ne ta hanyar rabe-rabe daidai da bin kariya daga cututtuka daga kowacce ƙasa.

 

Haka kuma Ma’aikatar tana bada shaidar tantancewa ga kamfanonin hidimomi da suka cancanta, amma daidai da yadda ake aiwatar da ayyuka da suka yi daidai da yanayin da ake ciki, da kuma kula da kariya ta lafiya

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here