YANZU-YANZU: Shugaban Ƙungiyar Masu Hada-hadar Hajji Ta Ƙasa Mai zaman kanta ya rasu

0
437

Shugaban Ƙungiyar Masu Hada-hadar Hajji Ta Ƙasa Mai zaman kanta(AHUON), Alhaji Salihu Butu ya rasu.

Har kafin rasuwarsa, Butu ya kasance shine shugaban AHOUN ɗin na riƙon ƙwarya.

Shawara don karantawa: Sanwo Olu zai ƙaddamar da Adashin Gata na Hajji a Legas

A dandalin kafar WhatsApp na ƴan jarida na Hukumar Aikin Hajji ta Ƙasa (NAHCON) a ka sanar da rasuwar ta sa.

Ya rasu yau juma’a a asibiti a garin Garki da ke Birnin Tarayya, Abuja.

Nan gaba kadan za a sanar da jana’izar sa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here