ABU ta ƙirƙiro da digirin-digirgir a kan hada-hadar aikin Hajji

0
456

 

 

 

Daga Mustapha Adamu

 

 

Cibiyar Karatu daga Nesa ta Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya ta ƙirkiro da shirin digiri na biyu a kan Gudanarwar Cinikayya (MBA), mai ɗauke da wani fanni na Hada-hadar Aikin Hajji.

 

Hajji Reporters ta gano cewa shirin, wanda za a riƙa yin karatun daga nesa, na ɗaya daga cikin sabbin fannonin karatu da ta ƙirƙiro kuma ya samu sahalewa daga Hukumar Gudanarwar Jami’o’i ta Ƙasa (NUC).

 

A wata ƙasida ta talla da wannan jarida ta samu, jami’ar ta ce duk masu sha’awar shiga shirin sai su buɗe shafin yanar gizo na www.apply.abudlc.edu.ng domin neman shiga shirin.

 

Sannan ta ce duk mai sha’awa sai ya tabbatar ya na da shaidar takaddun da a ke buƙata, sannan ya cika dukkan sharuɗɗan da ake buƙata kamar yadda a ka zayyano su a shafin yanar gizo na www.abudlc.edu.ng.

 

Sannan tallan ya ce ɗalibai za su riƙa samun darussan da a ke koyawa ta kafar yanar gizo a ko da yaushe

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here