Hajjreporters Ta Yiwa AHUON Ta’aziyyar Rasuwar Shugabanta na Ƙasa

0
488

 

Daga Jabiru Hassan, Kano

 

Ƙungiyar Ƴan Jarida Masu bada Rahotanni kan Aikinikin Hajji da Umara,  watau Independent Hajjreporters(IHR) ta nuna alhininta na rasuwar Alhaji Salisu Butu, Shugaban Ƙungiyar Masu Hada-hadar Aikin Hajji da Ummara na Ƙasa.

 

Haka kuma IHR ta miƙa saƙon ta’a ziyya ga iyalai, ƴan’uwa, AHOUN da kuma  Hukumar Hajji ta Ƙasa (NAHCON) bisa rasuwar Butu, wanda ya rasu Juma’ar da ta gabata.

 

A cikin wata sanarwa da shugaban IHR na ƙasa, Amir Ibrahim Mohammed ya sanya wa hannu ya kuma aka rabata ga manema labarai a ranar Lahadi, ƙungiyar ta nuna jimaminta na wannan babban rashi da akayi.

 

A cewar ƙungiyar, rashin Shugaban AHUON ɗin wani babban gibi ne ga fannin aikin Hajji da Umara a wannan ƙasa ta  Nijeriya da kuma duniya baki ɗaya.

 

Sannan  Hajj Reporters ɗin ta kuma miƙa wannan saƙo na ta’aziyya ga hukumomin kula da jin daɗin alhazai na jihohin kasarnan da dukkanin masu ruwa da tsaki kan aikin Hajji da Umara.

 

A ƙarshe, IHR na fatan Allah Ubangiji Ya gafartawa Alhaji Salisu Butu da dukkanin al’umar musulmin duniya baki ɗaya.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here